Newcastle United ta ziyarci Barcelona, domin wasa na biyu a Champions League ranar Laraba a Camp Nou.
A makon da ya wuce ƙungiyoyin biyu sun tashi 1-1 a St James Park, inda Newcastle ta fara cin ƙwallo daga baya Barcelona ta farke a bugun fenariti.
Wannan shi ne karo na biyu da za su kece raini a Champions League a bana, bayan da Barcelona ta ci Neewcastle 2-1 ranar 18 ga watan Satumba a Ingila.
Sai dai wannan ne karo na bakwai da za su kece raini a tsakaninsu, inda Barcelona ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya da Newcastle ta yi nasara ɗaya.
Sun fara haɗuwa a Champions League a kakar 1997/98, shi ne Newcastle ta fara da yin nasara 3-2 a cikin watan Satumba 1977.
Barcelona tana ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 70 da tazarar huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu.
Haka kuma Barcelona za ta karɓi bakuncin Rayo Vallecano a gasar La Liga ranar Lahadi a Camp Nou.
Newcastle mai fatan samun tikitin kwata fainal a gasar zakarun Turai tana ta tara a teburin Premier League da maki 42, wadda za ta yi wa Sunderland masauki ranar Lahadi a Premier League.