Super Falcons za ta fara da wasa da Brazil a Olympic 2024

Tawagar kwallon kafar mata ta Nigeria, Super Falcons za ta fara wasan a cikin rukuni da Brazil a gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci a bana.

Nigeria da Brazil za su fara fafatawa ranar Alhamis da yammaci 25 ga watan Yuli a filin wasa da ake kira Stade Matmut- Atlantique, Bordeaux, da ke France.

Kungiyar da Randy Waldrum ke jan ragama za ta buga karawar gaba ta biyu a cikin rukuni da Spain mai rike da kofin duniya ranar 28 ga watan Yuli a Stade de la Beujoire, Nantes.

Daga nan ne Super Falcons mai rike da kofin nahiyar Afirka tara za ta buga wasa na karshe na uku a cikin rukuni da Japan ranar Laraba 31 ga watan Yuli a dai Stade de la Beujoire, Nantes a France.

Super Falcons ta samu gurbin shiga gasar Olympic ta bana, bayan da ta ci South Africa 1-0 gida da waje.

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria ta samu gurbin shiga gasar Olympic, bayan da ta je ta tashi ba ci a South Africa ranar Talata. Latsa nan don ci gaba da karatu

Leave a comment