Super Falcons ta ci kwallaye da yawaa karon farko

Super Falcons ta caskara Cape Verde da ci 5-0 a wasan farko a neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta mata da za a yi a Morocco a badi.

Wannan shi ne karon farko da Nigeria ta dura kwallaye da yawa a raga a wasan mata, tun bayan wadda ta caskara Eguatorial Guine 6-0 a gasar cin kofin duniya a 2018.

Cape Verde da Super Falcons za su buga wasa na biyu ranar 5 ga watan Disamba a Estádio Nacional de Cabo Verde.

‘Yan wasan da Super Falcons ta gayyata:

Masu tsaron raga: Chiamaka Nnadozie (Paris FC); Tochukwu Oluehi (Shualat Alsharqia FC, Saudi Arabia); Christiana Obia (Edo Queens)

Masu tsaron baya: Osinachi Ohale (Pachuca FC, Mexico); Glory Edet (FCF TP Mazembe, DR Congo); Rihanat Kasali (Bayelsa Queens); Oluwatosin Demehin (Stade de Reims, France); Akudo Ogbonna (Remo Stars Ladies); Rofiat Imuran (Stade de Reims, France)

Masu buga tsakiya: Motunrayo Ezekiel (Rivers Angels); Esther Onyenezide (FC Robo Queens); Peace Efih (Sporting Club de Braga, Portugal); Rasheedat Ajibade (Atletico Madrid FC, Spain); Deborah Abiodun (University of Pittsburgh, USA); Toni Payne (Sevilla FC, Spain); Chioma Olise (Edo Queens)

Masu cin kwallaye: Omorinsola Babajide (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Chiamaka Chukwu (Rivers Angels); Esther Okoronkwo (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain); Uchenna Kanu (Racing Louisville, USA); Gift Monday (Coasta Adeje Tenerife Egatesa, Spain)

Leave a comment