Kwallon mata: Super Falcons ta ci Banyana Banyana a Abuja

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria ta yi nasara a kan ta Africa ta Kudu da ci 1-0 ranar Juma’a a filin wasa na MKO Abiola da ke babban birnin tarayya Abuja, Nigeria.

Sun kara ne a wasan farko na neman gurbin shiga gasar tamaula ta mata a Olympic da za a yi a Faransa cikin shekarar nan.

Super Falcons ta ci kwallon a minti na 42 ta hannun kyaftin Rasheedat Aajibade.

Ranar Talata za a buga wasa na biyu a Loftus Versfeld a Pretoria, domin neman gurbin shiga wasannin Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci.

Ranar Asabar Banyana Banyana ta koma Africa ta Kudu, yayin da Super Falcons za ta kai ziyara a daren Lahadi daga Lagos.

Leave a comment