Tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kara da ta Zimbabwe a wasa neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.
Wannan shi ne wasa na bibiyu da za a buga a cikin rukuni, inda Najeriya ta tashi 1-1 da Lesotho a Uyo ranar Alhamis.
Ita kuwa Zimbabwe ta tashi 0-0 da Rwanda a wasan farko a cikin rukuni na ukun da suka yi ranar Laraba.
Zimbabwe tana buga wasanninta a Rwanda, bayan da filayaenta ba wanda yake da darajar da ake bukata.
Tuni dai Super Eagles ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a buga a Ivory Coast daga Janairu zuwa Fabrairun 2024.
Super Eagles ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022, bayan da Ghana ta yi mata fancale.
Wasu wasannin da za a buga ranar Lahadi:
Burundi da Gabon
Mozambique da Algeria
Saliyo da Masar
Sudan da Jamhuriyar Congo