Super Eagles za ta kara da Mali a Morocco ranar Talata

Mai aikin rikon kwaryar kociyan Super Eagles, Finidi George zai kara jan ragamar tawagar wasan sada zumunta na biyu da Mali ranar Talata a birnin Marrakech a Morocco.

Ranar Juma’a Super Eagles ta yi nasarar cin Ghana 2-1 a dai wasan sada zumunta a Morocco.

To sai dai Nigeria za ta buga wasan ba tare da mai tsaron baya Calvin Bassey da mai buga tsakiya, Frank Onyeka ba, wadanda suka ji rauni.

Haka kuma tuni Super Eagles za ta buga wasan na sada zumunta ranar Talata ba tare da Victor Osimhen da Victor Boniface da mai tsaron baya, William Ekong da Olaoluwa Aina da Zaidu Sanusi.

Sauran da ba za su yi wi Super Eagles wasan ba sun hada da mai tsaron baya, Gabriel Osho da Tyronne Ebuehi da kuma Taiwo Awoniyi wadanda ke jinya.

Bayan da ‘yan wasan Super Eagles da yawa ke jinya hakan ya bai wa wasu damar da za su buga mata tamaula.

Wasu daga ‘yan wasan Super Eagles da za su buga mata fafatawar ranar Talata sun hada da mai tsaron raga, Olorunleke Ojo da mai tsaron baya Kenneth Omeruo da Jamilu Collins da mai buga tsakiya, Alhassan Yusuf da Nathan Tella da Sadiq Umar da kuma Fisayo Dele-Bashiru.

Leave a comment