Super Eagles ta fitar da ‘yan wasa 25 da za su buga mata Afcon 2024

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta bayyana ‘yan wasa 25 da za su buga mata gasar cin kofin Afirka da za a buga a 2024.

Cikin ‘yan wasan har da kyaftin Ahmed Musa, wanda aka kara gayyata, wanda bai buga wasa biyu a neman shiga gasar kofin duniya ba.

Cikin jerin ‘yan kwallon sun hada da masu tsaron raga uku da masu tsare baya tara da masu buga tsakiya biyar da ‘yan wasa takwas a gurbin masu cin kwallaye.

Fitatuu a gurbin masu cin kwallaye sun hada da Musa da Victor Osimhen da Kelechi Iheanacho da kuma Samuel Chukwueze.

Cikin masu tsare baya har da Kenneth Omeruo, wanda yana cikin ‘yan kwallon da Nigeria ta lashe kofin a 2013 da kuma William Ekong, wanda shi ne jagoran masu tsare bayan.

A fannin ‘yan wasan tsakiya har da Wilfred Ndidi, wanda bai yi wasa biyu ba a neman shiga gasar kofin duniya.

Sauran sun hada da Alex Iwobi da kuma Joe Ayodele-Aribo.

A kokarin da Super Eagles take na ganin ta taka rawar gani a gasar, za ta yi atisayen mako daya a Abu Dhabi daga 2 zuwa 9 ga watan Janairu.

Bayan nan tawagar za ta koma Nigeria, sannan ta je Ivory Coast daga 10 watan Janairu.

Super Eagles za ta fara wasa a rukunin farko ranar 14 ga watan Janairu da Equatorial Guinea.

Wasa na biyu kuwa za ta yi da mai masaukin baki Ivory Coast ranar 18 ga watan Janairu.

Za ta kammala karawar cikin rukuni da fafatawa da Guinea Bissau ranar 22 ga watan Janairu.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar 13 ga watan Janairu a Ivory Coast.

Jerin ‘yan wasa 25 na Super Eagles:

Masu tsare raga: Stanley Nwabili (Chippa United, South Africa); Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus); Olorunleke Ojo (Enyimba FC)

Masu tsare baya: Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Chidozie Awaziem (Boavista FC, Portugal); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce FC, Turkey); William Troost-Ekong (PAOK Salonika, Greece); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal); Kenneth Omeruo (Kasimpasa FC, Turkey); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal)

Masu buga tsakiya: Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Joe Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Fulham FC, England)

Masu cin kwallaye: Ahmed Musa (Sivasspor K, Turkey); Victor Osimhen (Napoli SC, Italy); Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Sadiq Umar (Real Sociedad, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Samuel Chukwueze (AC Milan, Italy); Victor Boniface (Bayer Leverkusen, Germany)

Leave a comment