Super Eagles ta dauki Finidi George sabon kociyanta

Hukumar kwallon kafa ta Nigeriya ta nada Finidi George a matakin sabon kociyan Super Eagles.

Ya maye gurbin Jose Peseiro Santos, wanda kwantiraginsa ya kare a karshen kammala gasar kofin Afirka da aka yi a Ivory Coast, wanda Super Eagles ta yi ta biyu a shekarar nan.

Mai shekara 53 ya yi aikin kocin rikon da tawagar Nigeria a wasan sada zumunta da ta ci Ghana 2-1 da rashin nasara 2-0 a Hannun Mali a Morocco a watan Maris.

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta bayar da sanarwar daukar George ranar Litinin, wanda ya taba horar da Enyimba International ta Nigeria.

George ya buga wa Super Eagles wasa 62 da lashe kofin Afirka a 1994 da zuwa gasar kofin duniya a shekarar a Amurka da halartar gasar kofin duniya da aka yi a 2018.

An bai wa kociyan wuka da nama, domin ya kai Nigeria gasar kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026.

Nigeria, wadda take ta uku a rukuni na uku za ta kara da Afirka ta Kudu cikin watan Yuni da kuma Benin a wasannin neman shiga gasar kofin duniya.

Cikin wadanda George ya yi takara da su a neman kociyan Super Eagles sun hada da Emmanuel Amuneke da dan kasar Spain, Domenec Torrent da mai horar da Manchester City, Pep Guardiola

Sai dai NFF ba ta fayyace kunshin yarjejeniyar da ta kulla da George ba.

Leave a comment