South Afirka ta hakura da zawarcin kofin duniya na mata na 2027

Afirka ta Kudu ta hakura da neman izinin karar bakuncin gasar kofin duniya ta mata da za a yi a 2027.

Kasar ta ce lokaci ya kure mata ba za ta iya gabatar da tsare-tsaren yadda za ta gudanr da wasanni a gaban Fifa cikin Disamba ba.

Ranar 8 ga watan Disamba ita ce ranar karshe ta mika takara, mahukuntan Afirka ta Kudu sun ce za su tara a gasar kofin duniya ta mata ta 2031.

Da yake yanzu Afirka ta Kudu ta janye daga takara, wadanda aka bari kawo sun zama su uku.

Cikinsu har da hadaka tsakanin Belgium da Netherlands da kuma Germany sai Mexico da United States da kuma Brazil mai son karba ita kadai.

Ranar 17 ga watan Mayun 2024 a babban taron Fifa za a fayyace, wadda za a bai wa takarar gasar kofin duniya ta mata a 2027.

Australia da New Zealand ne suka gudanar da gasar da aka yi a 2023, wadda duk bayan shekara hurhudu ake kece raini.

Spain ce ta lashe kofin, bayan da ta ci England 1-0 a gaban ‘yan kallo 75,784 a Sydney cikin watan Agusta.

Leave a comment