Slot ya ce yana son karbar aikin horar da Liverpool

Kociyan Feyenoord, Arne Slot ya ce yana son karbar aikin mai horar da Liverpool, domin maye gurbin Juergen Klopp a kakar badi.

Kociyan dan kasar Netherlands ya sanar da hakan ranar Alhamis, ya kara da cewar yana fatan kungiyarsa da mai buga Premier League za su kai ga cimma kwantiragi.

Ranar Laraba, jaridun Netherlands suka wallafa cewar Liverpool ta fara tattaunawa da da mai rike da Eredivisie, domin daukar Slot ya maye gurbin dan kasar Jamus, wanda zai ajiye aiki da zarar an kammala kakar nan.

Slot mai shekar 45, yana da kunshin yarjejeniyar da za ta kare a kungiyar Rotterdam zuwa karshen kakar 2026.

A bara an yi ta alakanta kociyan da zai koma Tottenham, amma ya yanke shawarar ci gaba da jan ragamar Feyenoord.

Ana jinjinawa kociyan wajen salon kai hare-hare da ya dora Feyenoord, wadda ya ja ragama ta lashe lik a 2023 da kuma KNVB Cup ranar Lahadi.

A kakarsa ta farko, Slot ya kai Feyenoord, kungiyar Rotterdam wasan karshe a sabon kofin da aka kirkira Europa Conference League.

Cikin watan Janairu Kloop ya sanar zai ajiye aikin horar da Liverpool, domin yana bukatar hutuwa, bayan shekara tara kan aikin.

Dan kasar Jamus ya ja ragamar Liverpool ta dauki Champions League da Premier League da Club World Cup da FA Cup da League Cup da kuma Super Cup.

Leave a comment