Shin me Ali Kanin Bello ke yi a wannan watan na Azumi?

Yanzu dai ba inda ake yin damben gargajiya, saboda watan Azumi, inda ake sa ran ci gaba da fafatawa da zarar an yi Sallah Karama.

Tun daga ranar da aka ce an sauke Azumi ake fara kakar dambe har sai wani Azumin mai zuwa kafin a sake yin hutun wata ɗaya, kenan ana yin wasa a kowacce rana tsawon wata 11.

Ali Kanin Bello Sarkin dambe ɗan mutan Gyalange ya koma gida, inda yake kiwo da noma, daman shi mahauci ne yana zuwa kasuwa, sannan yana gudanar da ibada.

Da zarar an kammal Azumi, sai ya dawo ya ci gaba da wasan, kuma tun yanzu masu gidajen dambe na yi masa tayin zuwa ya buga musu wasanni da zarar an sallata.

Saboda haka shi ne zai zaɓi tayi mai tsoka daga cikin masu zawarcinsa – yayin da ake sa ran za a yi damben motar Gwamnan Kano da zarar baki ya buɗe.

Shin wane gidan damben kuke tunanin Ali Kanin Bello zai fara wasa da zarar an yi karamar Sallah? Ku rubuta mana ra’ayinku.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top