Shin ko PSG za ta dauki fansa kan Newcastle?

Ranar Talata Paris St Germain za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan Champions League.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyin za su hadu a tsakaninsu, bayan wanda Newcastle ta ci 4-1 a St James Park ranar 30 ga watan Oktoba.

Sai da Newcastle ta fara dura kwallo uku a ragar PSG ta hannun Miguel Almiron da Dan Burn da kuma Sean Longstaff a wasan farko da suka kara.

Daga baya ne Lucas Hernandez ya farkewa PSG daya, daga baya Newcastle ta kara na hudu.

Dortmund ce ta daya a rukuni na shida da maki bakwai, sai PSG ta biyu da maki shida.

Milan ce ta uku da maki biyar, sannan Newcastle ta karshe mai maki hudu, baya da za a buga fafatawa ta biyar-biyar.

Paris St Germain ba ta taba dauka Champions League ba, dalilin da ya sa ta dauki Neymar da Lionel Messi. Duk da haka kungiyar ba ta samu damar lashe kofin zakarun Turan ba, wadda Neymar ya koma buga gasar Saudi Arabia, Messi ya koma Inter Miami ta

Leave a comment