Shagon Kosilaye ya kashe Abba Shagon Roget a damben gwamna

Shagon Kosilaye ya kai zagaye na biyu a gasar gwamnan Kano, bayan da ya doke Abba Shagon Roget.

Shagon Kosilaye daga Kudu ya saka wando ja yayin da Abba Shagon Roget mai wanda ruwan bula ya wakilci Arewa.

Wasan na su bai wani dauki lokaci ba domin cikin turmin farko aka kare a filin wasa na Aado Bayero Square a Kano, Nigeria ranar Asabar.

Za a ci gaba da gumurzu ranar Lahadi, inda Garkuwan Cindo ya sauka a Kano ranar Asabar domin shiga gasar da za a lashe naira miliyan biyu.

Sakamakon wasannin damben gwamna da aka buga ranar Asabar

  • Shagon Dogon Inda daga Arewa ya doke ya buge Autan Korona daga Kudu
  • Autan Bahagon Balangada daga Jamus ya buge Dogon Korona daga Kudu
  • Bahagon Dage daga Kudu ya yi nasara a kan Mola-Mola daga Arewa wanda ya ji rauni
  • Dogon Dogon Sani daga Arewa ya buge Kurtun Shagon Mada daga Kudu
  • Shagon Gwagwarwa daga Arewa ya buge Shagon Alhazai daga Jamus
  • Shagon Kosilaye daga Kudu ya doke Abba Shagon Roget daga Arewa

Leave a comment