Saura kwallo daya Salah ya ci na 150 a Premier

Ranar Asabar Manchester City za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 13 a gasar Premier League.

Kawo yanzu Erling Haaland, wanda aka ce ya yi atisaye a City yana da kwallo 13 a raga a bana, sai Mohamed Salah mai 10.

Haaland ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Norway wasan sada zumunta, wanda ake cewa da kyar idan zai yi karawa da Liverpool.

To sai dai dan kwallon Masar mai shekara 31 ya ci 149 a Premier League a Liverpool tun daga kakar 2017/18.

Salah, wanda ya buga wa Liverpool wasa 243 a lik, an ci wasa 156 da shi a fili da rashin nasara a karawa 33.

Cikin kwallayen da ya ci har da takwas da kai da 22 da kafar dama da 119 da hagu da kuma 23 a bugun fenariti.

Salah, wanda zai wakilci Masar a gasar cin kofin Afirka a Ivory Coast a 2024 ya buga kwallo zuwa raga sau 864, amma 373 ne suka nufi raga kai tsaye.

Haka kuma ya buga kwallo ya bugi turke sai 20 da barar da dama 118, wanda aka bai wa katin gargadi takwas.

Dan wasan gwarzon dan kwallon Afirka karo biyu, ya yi laifi karo 120 da satar gida sau 117

Leave a comment