Saudi Arabia za ta karbi bakuncin gasar zakarun Asia

Saudi Arabia za ta karbi bakuncin wasan gasar zakaru ta Asia har karo biyu a jere.

Hukumar kwallon kafar Asia ce ta sanar da bai wa Saudi Arabia damar nan, wadda take fatan karbar bakuncin kofin duniya.

Gasar da za a yi tsakanin kungiyoyi 12 a badi za ta maye gurbin wadda ake yi tun farko.

Duk wadda ta lashe kofin za ta karbi ladan dalar Amurka miliyan 12.

Za a raba kungiyoyi gida biyu dauke da 12 kowanne ta yadda za su buga gida da waje don tantance wadanda za su buga zagayen gaba.

Daga nan guda takwas za su kai matakin quarter finals daga nan ta kai da matakin daf da karshe da wasan karshe, shi ne wanda Saudi Arabia za ta shirya a kakar 2024-25 da kuma ta 2025-26.

Saudi Aarabia ta samu damar nan, bayan da ta yi takara da Iraq.

Saudi Arabia ce kadai ke takarar neman izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi a 2034.

Haka kuma kasar ce za ta shirya wasannin FIFA Club World Cup cikin Disamba da 2027 Asian Cup da kuma 2034 Asian Games.

Leave a comment