Sancho baya fatan ya koma Man United bayan kakar bana

Chelsea na son sayen dan kwallon Napoli, Victor Osimhen, wanda aka gindaya kudin sayar da shi £100m idan yarjejeniyarsa bai kare ba. (Sky Italia)

West Ham United da Tottenham suna daga gaba masu son daukar dan kwallon Brentford, Ivan Toney, wanda suke fatan taya shi £50m. (Football Transfers)

Viktor Gyokeres, bai amince ya tsawaita kwantiraginsa ba a Sporting Lisbon bayan da Arsenal ke son yin zawarcinsa. (Standard)

Darwin Nunez yana daga cikin ‘yan wasan da Barcelona za ta yi kokarin dauka daga Liverpool, domin ya maye gurbin Robert Lewandowski, 35. (Sun)

Jadon Sancho, baya fatan komawa Manchester United a karshen kakar nan, bayan wasannin aro da yake yi a Borussia Dortmund. (Talksport)

Chelsea za ta kara kaimi wajen zawarcin dan wasan Shakhtar Donetsk, Georgiy Sudakov kan £65m wanda Arsenal da Manchester City da kuma Liverpool ke bibiyar dan kwallon. (Mail)

Dan wasan Atletico Madrid, Jan Oblak, yana cikin wadanda Chelsea ke son dauka don kara karfin kungiyar a kakar badi. (Fichajes)

Arne Slot, wanda zai maye gurbin Jurgen Klopp at Liverpool daga Feyenoord zai koma Netherlands, domin dauko dan wasa Mats Wieffer da kuma Lutsharel Geertruida. (Football Insider)

Sevilla tana daga cikin kungiyoyin dake bibiyar dan wasan Leicester City, Enzo Maresca, wanda ya bayar da gudunmuwar da kungiyar ta koma gasar Premier League. (Mail)

Leave a comment