Mohamed Salah zai bar Liverpool da zarar an kammala kakar bana, kamar yadda É—an wasan na Masar ya bayyana.
Salah ya koma Liverpool daga AS Roma a shekarar 2017, kuma ya sanar da shirin barinsa ne ta shafukan sada zumunta.
Rahotanni sun nuna cewa Liverpool da Salah sun cimma yarjejeniya ta soke kwantiragin da ya rage a tsakaninsu, duk da cewa a watan Afirilu 2025 ya sabunta kwantiraginsa na wasu shekaru biyu.
A kakar bana, Salah ya ci ƙwallaye 10 a wasanni 34 a dukkan gasa, wanda ke nuna raguwar yawan ƙwallayen da yake ci idan aka kwatanta da shekarun baya.
Guardiola ya zama na farko da ya ci Carabao Cup biyar
Bayern ta bai wa Dortmund tazarar maki tara
Tun a baya an yi ta hasashen barinsa a watan Janairu, amma ya ci gaba da taka leda bayan gasar AFCON 2025 da aka gudanar a Morocco.
Salah ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da Liverpool ta samu, ciki har da lashe:
- Premier League biyu
- UEFA Champions League
- FIFA Club World Cup
- UEFA Super Cup
- FA Cup
- EFL Cup sau biyu
- Community Shield
A tsawon zamansa a Liverpool, Salah ya zura ƙwallaye 255 a wasanni 435, wanda ya sa ya zama na uku a tarihin masu yawan cin ƙwallaye a ƙungiyar, bayan Ian Rush (346) da Roger Hunt (285).
Haka kuma, Salah ya lashe takalmin zinare na Premier League sau huɗu, tare da samun kyautar fitaccen ɗan wasa na ƙwararrun ƴan wasa sau uku (2018, 2022 da 2025).
A halin yanzu, Liverpool tana matsayi na shida a teburin Premier League, yayin da ake saura wasanni bakwai a kammala kakar bana.
Liverpool za ta fafata da Paris Saint-Germain a zagayen kwata fainal na Champions League, sannan ta buga da Manchester City a FA Cup zagayen Æ´an takwas ranar Asabar 4 ga watan Afirilu.