Salah ya kafa tarihi a wasan Tottenham a Premier

Liverpool ta doke Tottenham 4-2 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Anfield.

Mohamed Salah ne ya fara cin kwallo, sai Andrew Robertson ya kara na biyu, sannan Cody Gakpo ya ci na uku da kuma Harvey Elliott da ya zura na hudu a raga.

Tottenham ta zare biyu ta hannun Richarlison da kuma Hueng Son-Min a wasa na hudu a jere da aka doke kungiyar da Ange Posteglou ke jan ragama.

Kwallon da Salah ya ci shi ne na 18 a Premier a bana, kuma shi ne bai ba Elliot ya zura na hudu a raga a wasan na hamayya.

Kenan mai shekara 31 ya ci kwallo sama da 10 ya bayar da 10 aka zura a raga a kaka ta uku a jere a Premier League.

Tsohon dan wasan Chelsea ya zura 19 a bara ya kuma bayar da 12 aka ci a kakar da ta gabata.

Sai dai kwallo biyar ya bayar aka zura a raga shi kuma ya ci sama da 10 a kakar 2020/21, amma a 2019/20 ya ci kwallo 19 ya bayar da 10 aka zura a raga.

A kakar farko da ya fara buga wa Liverpool tamaula a 2017/18 ya ci kwallo 32 ya bayar da 10 aka zura a raga.

Tsohon dan wasan Manchester United, Wayne Rooney shi ne kadai ya ci kwallo fiye da 10 ya kuma bayar da sama da 10 aka zura a raga a kaka biyar a Premier League.

Leave a comment