salah ya ci brentford kwallo biyu a anfield

Liverpool ta hada maki 27 tana mataki na biyu a teburin Premier League iri daya da na Arsenal ta uku da Manchester City ta daya.

Liverpool ta doke Brentford 3-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Anfield.

Dan wasan tawagar Masar, ya ci kwallo 12 a Premier a bana, tara daga ciki a Anfield ya zura a raga, bayan da kungiyar ke taka rawar gani a kakar bana.

Kwallo taran da Salah ya ci Darwin Nunez ne ke bashi kwallon a Anfield, kuma shi ne ya bai wa Salah da ya zura a ragar Brentford a ranar Lahadi.

Diego Jota ne ya ci na uku saura minti16 a tashi daga karawar, sai dai City za ta iya ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier idan har ba a doke ta ba a gidan Chelsea.

Chelsea na karbar bakuncin City a wasan mako na 12 a gasar Premier League a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Leave a comment