Salah ne ɗan Afirka kan gaba a cin ƙwallaye a Champions League

Mohammed Salah ya zama kan gaba a cin ƙwallaye daga Afirka a Champions League.

Ranar Laraba Liverpool ta doke Galatasaray 4-0 a Anfield a wasa na biyu a gasar zakarun Turai.

Kenan ta kai kwata fainal da cin 4-1 gida da waje kenan, bayan da aka doke ta 1-0 a wasan farko.

Cikin waɗanda suka ci mata ƙwallayen sun haɗa da Szoboszlai da Ekitiké da Gravenberch da Mohamed Salah.

Wadda ɗan kasar Masar ya ci, ita ce ta 50 jimilla shi ne kan gaba a cin ƙwallaye a Champions League daga Afirka.

Wanda yake na biyu shi ne Didier Drogba mai 44 tsohon ɗan wasan Chelsea da tawagar Ivory Coast.

Sauran sun haɗa da Samuel Eto’o ami 30, Sadio Mane mai 27 da kuma Riyad Mahrez mai 20 a raga.

Jerin ƴan wasan Afirka da ke kan gaba a cin ƙwallaye a Champions League:

  1. Mohammed Salah ƙwallo 50
  2. Didier Drogba mai 44
  3. Samuel Eto’o mai 50
  4. Sadio Mane mai 27
  5. Riyad Mahrez mai 20
  6. Pierre-Emerick Aubameyang mai 20
  7. Serhou Guirassy mai 18
  8. Seydou Doimbia 15
  9. Victor Osimhen 15
  10. Vincent Aboubakar mai 14

Wasu karin batutuwan da ya kamata ku sani

Mohammed Salah ya ci ƙwallayensa da yawa a Liverpool da wasu a Basel da kuma Roma.

Drogba ya zura 44 a raga a Champions League daga karawa 92.

Samuel Eto’o ya lashe Champions League uku, kuma shi ne na uku a Afirka a cin ƙwallaye a Champions League.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top