Sadio Mane ya yi bikin buga wa Senegal wasa na 100

Ranar Asabar Sadio Mane ya buga wa Senegal wasa na 100 a karawar da ta doke South Sudan 4-0.

Sun buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 da Amurka da Canada da Mexico da za su karbi bakuncin wasannin.

Tsohon dan wasan Liverpool, mai taka leda a gasar Saudi Arabia ya ci biyu a karawar rukuni na biyu, daga baya aka canje shi.

Hakan ya sa Senegal, mai rike da kofin nahiyar Afirka tana ta daya a rukunin, yayin da Jamhuriyar Congo ke ta biyu.

Za a ci gaba da wasa na bibiyu a cikin rukuni ranar Lahadi, wasu daga tawagogin da za su kara har da Algeria da Jamhuriyar Congo da Masar da Najeriya daga fafatawa 10 da za a buga.

Leave a comment