Rublev zai buga Hong Kong Open a 2024

Andrey Rublev zai buga Hong Kong Open a 2024 a gasar kwallon tennis a karon farko bayan shekara 20.

Hukumar kwallon tennis ta duniya ce ta sanar da cewar, wanda yake na biyar a jerin wadanda ke kan gaba a wasan zai je wasannin badin.

Mai shekara 26 dan kasar Rasha, zai shiga gasar tare da Tiafoe da Karen Khachanov.

Za a fara wasannin daga 1 zuwa 7 ga watan Janiaru a Victoria Park, gas ace ta shirin shiga Australian Open.

Wasan karshe da maza suka fafata a gasar tun 2002, kuma fitattu da suka lashe gasar sun hada da Pete Sampras da Andre Agassi da Pat Cash da Ivan Lendl da kuma Jimmy Connors.

Zakakuri dan kasar Australia, Rod Laver shi ne ya fara lashe gasar farko a 1973.

Leave a comment