Ronaldo ne kan gaba mafi karbar albashi a duniya

Cristiano Ronaldo ne kan gaba a jadawalin Forbes a matakin, dan wasan dake kan gaba a karbar albashi karo na hudu a jere, yayin da Jon Rahm ya koma na biyu.

Ronaldo dai shi ne na daya a bara a matakin mafi karbar albashi a tsakanin ‘yan wasa, sakamakon da ya koma taka leda a gasar Saudi Arabia a kungiyar Al Nassr.

Mujallar ta Forbes ta ce dan kwallon mai shekara 39 dan wasan tawagar Portugal na karbar $260m (£205m) – kari daga $136m (£108.7m) – fiye da shekara daya.

Abokin Ronald0 a hamayya wato Lionel Messi ya yi kasa zuwa mataki na uku biye da Rahm.

Rahm dan kasar Spain mai wasan kwallon golf ya samu ci gaba ne, bayan da ya koma buga gasar da Saudi ke daukar nauyi wato LIV Golf tour wanda ya hada $218m (£172m).

Haka kuma masu taka leda Neymar da Karim Benzema suna cikin ‘yan 10 farko, sakamakon da suka koma taka leda a Saudi Arabia.

Wanda yake na biyar shi ne Giannis Antetokounmpo kafin nan mai buga kwallon kwandon Amurka, basketball, LeBron James yana na hudu, yayin da takwaransa Stephen Curry ke mataki na tara, inda mai buga kwallon zari ruga ta Amurka, Lamar Jackson shi ne na 10.

Kamar yadda Forbes ta sanar wannan kididdigar ta hada da kudin da dan wasa ke samu da ya kai $1.38 bn (£1.06bn) kafin a cire haraji da kudin eja cikin wata 12 , kuma shi ne samu mafi tsoka a tarihi.

Jerin ‘yan wasa 10 dake kan gaba a karbar albashi a 2024

1. Cristiano Ronaldo, Kwallon kafa: $260m (£205m)

2. Jon Rahm, Kwallon golf: $218m (£172m)

3. Lionel Messi, Kwallon kafa: $135m (£107m)

4. LeBron James, Kwallon kwandon Amurka: $128.2m (£101m)

5. Giannis Antetokounmpo, Kwallon kwandon Amurka: $111m (£88m)

6. Kylian Mbappe, Kwallon kafa: $110m (£87m)

7. Neymar, Kwallon kafa: $108m (£85m)

8. Karim Benzema, Kwallon kafa: $106m (£84m)

9. Stephen Curry, Kwallon kwandon Amurka: $102m (£80m)

10. Lamar Jackson, Kwallon zari ruga ta Amurka: $100.5m (£79m)

Leave a comment