Rodri ya ce yana bukatar hutu a cikin kakar nan

Dan wasan Manchester City, Rodri yana yana tsara yadda zai hutu a kakar nan, bayan da kungiyarsa ke fatan kare lashe uku karo na biyu a jere.

Mai shekara 27 ya buga wa City wasa na 41 a Champions League da suka tashi 3-3 a Real Madrid zagayen Quarter finals ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Wasan da City ta tashi 3-3 a gidan Real shi ne kwana 429 wato fafatawa ta 66 tun bayan da kungiyar Etihad ta yi rashin nasara a karawar da Rodri ya buga mata tamaula a dukkan fafatawa.

‘Yan kwallo uku ne ke gaban Rodri a buga wasannin da yawa, kuma dukkansu masu tsaron raga ne.

Wasa hudu ne Rodri bai buga ba a bana sakamakon hukuncin dakatarwa, kuma dukkan karawar hudu an doke kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama.

Ranar Asabar Manchester City za ta kara da Luton Town a Premier League daga nan ta fafata da Real Madrid a Etihad a wasa na biyu a Champions League zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Laraba 17 ga watan Afirilu.

Daga nan City za ta fuskanci Chelsea a FA Cup karawar daf da karshe, sai ta je gidan Brighton ta kuma kara da Nottingham Forest a Premier League, sannan a fada watan Mayu.

A kakar da ta wuce City ta lashe FA Cup da Premier League da kuma Champions League.

Kungiyar Etihad tana ta ukun teburin Premier League da maki 70 da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta iyu da kuma Arsenal mai jan ragama.

Leave a comment