Ɗan wasan tsakiya na Manchester City da tawagar Spain national football team, Rodri, ka iya komawa Real Madrid a kakar baɗi, domin ci gaba da taka leda a ƙasar Spain.
Kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 29 zai kare a ƙarshen kakar wasa mai zuwa, wanda hakan ke nufin zai iya fara tattaunawa da sauran ƙungiyoyi bayan kammala kakar bana.
Rodri ya koma Manchester City daga Atlético Madrid a shekarar 2019, inda ya buga wasanni 293 kawo yanzu a ƙungiyar Etiahd.
A cewarsa, babu wani ɗan wasa da Real Madrid za ta nema ya ce ba zai je ba, yana mai ƙara da cewa yana da burin dawowa taka leda a gasar La Liga nan gaba.
Rodri, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a 2024, ya bayyana cewa zai duba yiwuwar komawa Real Madrid idan damar hakan ta samu.
Ɗan wasan tsakiya ya lashe kofi 12 tare da Manchester City, ciki har da Premier League huɗu da kuma gasar UEFA Champions League.
A kakar bana, Rodri ya buga wasa 18 kacal a gasar Premier League, bayan da ya samu rauni a ƙafarsa a shekarar 2024.
Haka kuma, Rodri ya buga wa Spain wasa 59, kuma yana cikin jerin ƴan ƙwallon da aka gayyata domin buga wasannin sada zumunta da Serbia da Egypt.
Ɗan wasan na fatan wakiltar ƙasarsa a gasar FIFA World Cup, bayan da ya taimaka wajen lashe UEFA European Championship a 2024 da kuma Nations League.
