Real za ta kara da Bayern a Champions League

Real Madrid za ta fafata da Bayern Munich a gasar zakarun Turai ta Champions League zagayen daf da karshe.

Kungiyar Spain ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da Manchester City a bugun fenariti da cin 4-3, wadanda suka tashi 1-1 har da karin lokacin a Etihad ranar Laraba.

A wasan farko a makon jiya ranar Talata, kungiyoyin biyu sun tashi 3-3 a Santiago Bernabeu, kenan Real ta dauki fansa kamar yadda City ta fitar da ita a bara a gasar ta zakarun Turai.

Ral ce za ta fara ziyarta Bayern a wasan farko a daf da karshe ranar 30 ga watan Mayu ko kuma 1 ga watan Afirilu, sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 7 ko kuma 8 ga watan Afirilu a Santiago Bernabeu.

Real Madrid da Bayern Munich sun fuskanci juna karo 26 a gasar zakarun Turai, bayan da Real keda Champions League 14, Bayern tana da shida.

Wasa na karshe da suka kara a bayan nan shi ne a daf da karshe a 2017/18, inda Real Madrid ta kai wasan karshe ta kuma lashe kofin.

A kakar nan Bayern Munich ta yi ta daya a rukunin farko, wadda ta ja ragamar Copenhagen da Galatasaray da kuma Manchester United, inda ta yi waje da Lazio a zagayen ‘yan 16 da cin (3-1) gida da waje da fitar da Arsenal a quarter-finals (3-2) gida da waje.

Leave a comment