Real za ta bayyana daukar Mbappe bayan Champions League

Real Madrid za ta jira har sai bayan Champions League da za ta kara da Borussia Dortmund ranar 1 ga watan Yuni, kafin ta sanar da daukar Kylian Mbappe. (Athletic – subscription)

Manchester United za ta kara kokarin taya dan wasan Barcelona, Frenkie de Jong, wanda aka ki sayar mata da shi a 2022. (Mundo Deportivo – in Spanish).

Arsenal ta ci karo da cikas a kokarin daukar Martin Zubimendi, bayan da kociyan Real Sociedad, Imanol Alguacil ya ce ba zai sayar da dan wasan ba.. (Metro)

Kungiyar dake buga gasar Saudi Pro League, wadda ta lashe kofin bana, Al-Hilal za ta yi kokarin taya dan wasan Tottenham, Richarlison da zarar an kammala kakar nan.. (Mail)

Napoli na fatan daukar dan wasan Tottenham, Radu Dragusin, wanda ya koma England da taka leda, yayin da Tottenham ke bukatar sayar da shi kan £40m. (Sun)

Dan wasan Barcelona, Raphinha zai iya barin kungiyar a bana, amma sai idan an yi zawarcinsa daga wata kungiya a Premier League club. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Bayern Munich ta nuna aniyar daukar kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner domin maye gurnin Thomas Tuchel, sai dai abon kociyan ya ce zai ci gaba da jan ragamar kungiyar Selhurst Park. (Sky Sports)

Leave a comment