Manchester City ta yi ban kwana da Champions League na bana, sakamakon da Real Madrid ta fitar da ita da cin 5-1 gida da waje.
Ranar Talata ƙungiyar Spaniya ta je Etihad ta ci Manchester City 2-1 a wasa na biyu a gasar da aka bai wa Bernardo Silva jan kati tun a minti na 20 da take leda.
Real Madrid ta ci ƙwallayen ta hannun Vinicius Junior ta farko a bugun fenariti, yayin da Erling Haaland ne ya ci wa City ƙwallon ta tilo.
Wannan shi ne karo na 17 da suka fuskanci juna a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Real Madrid ta yi nasara bakwai da canjaras biyar, City ta ci biyar daga ciki.
A wasan farko da suka buga a makon jiya a gasar ta zakarun Turai a Sifaniya, Real ce ta yi nasara 3-0, kenan ta kai zagayen kwata fainal da cin 5-1 gida da waje.
Real ta kai zagayen ƴan 16 ne tun farko bayan fitar da Benfica, ita kuwa City ta kai zagaye na biyu kai tsaye a Champions League.
Da wannan sakamakon watakila Real Madrid ta fuskanci Bayern Munich a zagayen ƴan takwas, bayan da ƙungiyar Jamus ta sharara 6-1 a ragar Atalanta, waɗanda za su buga wasa na biyu ranar Laraba.
Kenan watakila Bayern Munich ta ɗauki fansa a kan Real Madrid, wadda ta fitar da wadda take ta ɗaya a teburin Jamus karo bakwai a Champions League.
Yanzu dai abinda ya rage a gaban City shi ne wasan karshe a Carabao Cup da Arsenal ranar Lahadi 22 ga watan Maris a Wembley.
Haka kuma City tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki tara tsakani da Arsenal, wadda ke jan ragama.