Real Madrid ta koma matakin farko a LaLiga

Rodrygo ya ci gaba da taka rawar gani a Real Madrid, wadda ta doke Granada 2-0 ranar Asabar a Santiago Bernabeu

Wasa ne na mako na 15 a gasar Spain da Real Madrid ta koma matakin farko, bayan da Girona ta karba na dan rikon kwarya.

Girona ce ta fara wasa ranar Asabar a LaLiga, wadda ta yi nasara a kan Valencia da cin 2-1, daga baya Real ta karbe gurbin.

Brahim Diaz ne ya fara ciwa Real Madrid kwallo tun kan hutu, daga baya Rodrygo ya zura na biyu a raga a zagaye na biyu.

Kawo yanzu dan wasan tawagar Brazil ya ci kwallo bakwai a wasa biyar baya da ya buga a dukkan karawa a bana.

Real Madrid ta buga karawar bayan da ‘yan wasan ta da dama ke jinya, ciki har da Thibaut Courtois da Vinicius Junior.

Amma hakan bai hana Real Madrid ta doke Granada ba, wadda take ta 19 a kasan teburin LaLiga.

Jude Bellingham ya buga wasan, amma bai samu cin kwallo ba, wanda ya kai hari har 11 a fafatawar.

Ranar Lahadi Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan mako na 15 a LaLiga.

Atletico Madrid ce ta uku a teburin LaLiga da maki 31, iri daya da na Barcelona, wadda take ta hudu.

Leave a comment