Real Madrid ta kara nutsa Granada kasan teburin La Liga

Real Madrid ta doke Granada 4-0 a wasan mako na 36 a La Liga da suka kara ranar Asabar, saura wasa bibiyu a kammala kakar bana.

Real ta fara cin kwallo ta hannun Francisco Garcia, sannan Arda Guler ya kara na biyu daga baya Brahim Diaz ya ci biyu a fafatawar.

Tun kan Real Madrid ta buga wasan Granada ta fadi daga La Liga ta bana, bayan da Real Mallorca ta doke Las Palmas 1-0 tun da ranar Asabar.

Tun a makon jiya Real Madrid ta lashe La Liga na kakar nan, kuma na 36, jimilla ita ce kan gaba a yawan daukar kofin a tarihi.

Ita kuwa Granada tana ta biyun karshe a teburin babbar gasar tamaula ta Spain, yanzu za ta koma gasa mai daraja ta biyu.

Tuni kuma Real Madrid ta kai wasan karshe a Champions League, bayan da ta doke Bayern Munich 4-3 gida da waje.

Real Madrid mai Champions League 14 za ta fafata da Borussia Dortmund mai guda a wasan karshe ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Dortmund ta kai wasan karshe a gasar zakarun Turai ta bana, bayan da ta yi nasara 2-0 a kan Paris St Germain gida da waje.

Za a buga wasan karshe a Wembley ba tare da wata kungiya daga England ba, bayan da Real ta fitar da Manchester City, sai Bayern Munich ta yi waje da Arsenal a zagayen daf da na kusa da na karshe.

Leave a comment