Real Madrid ta gindaya wa’adin daukar Mbappe

Kungiyar Real Madrid ta gindayawa Kylian Mbppe lokacin da zai kulla yarjejeniyar komawa kungiyar da taka leda.

Har yanzu ana batun makomar dan kwallon, wanda aka tabbatar da ba zai bai tsawaita zamansa a Paris St Germain.

Hakan na nufin zai iya zuwa Real Madrid da zarar an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta Turai.

Tun a kakar 2022 Real Madrid ta so sayen dan wasan tawagar France, amma sai kawai aka ji ya tsawaita zamansa a PSG.

Kamar yadda AS ta wallafa, Real Madrid ta kwan da sanin cewar Mbappe ba zai tsawaita yarjejeniyarsa ba a PSG.

Amma ba za ta sake sakacin da ta yi a 2022 ba, lokacin da ta kwallafa rai, amma ciniki bai kammalu ba.

Tuni dai Real Madrid ta tsayar da ranar 15 ga watan Janairu, domin Mbappe ya kulla kwantiragi, idan hakan bai yiwuba, sai ta koma neman wani dan kwallon.

Rahoton ya ce idan Real Madrid ba ta samu daukar Mbappe ba, za ta mayar da hankali wajen sayo Erling Haaland daga Manchester City.

An fahimci cewar Real Madrid ta tanadi kudin sayen Haaland, domin ta magan ce gurbin mai cin kwallo a kungiyar.

Ana cewa kudin sayen Haaland dan kwallon tawagar Norway mai shekara 23, zai kai €200m.

Kudin da Man City ta gindaya ga duk kungiyar da take son sayen dan wasan idan yarjejeniyarsa bai kare ba ya kai £175m.

Leave a comment