Real Madrid ta fara shirin zuwa Manchester City

Real Madrid ta fara shirin zuwa Etihad domin buga wasa na biyu da Manchester City zagayen quarter finals ranar Laraba.

Kungiyoyin biyu sun tashi 3-3 a wasan farko a Spain a gasar zaakarun Turai, bayan da City ce ta fitar da Real a bara a gasar zakarun Turai har ta kai ga lashe kofin na farko a tarihi.

‘Yan wasan Real Madrid gabaki daya sun yi atisaye, sannan wadanda suka ci mata wasan Mallorca suma sun motsa jiki.

Haka kuma sun yi wasa da tamaula da raba kwallo a dan karamin fili, sai aaaaka dunga neman raga.

Har yanzu Courtois da Alaba na atisaye domin murmurewa daga raunin da suke jinya.

Real Madrid tana da Champions League 14 da ta dauka jimilla, ita ce kan gaba a wannan bajintar.

Haka kuma ranar ta Laraba Arsenal za ta je gidan Bayern Munich domin buga wasa na biyu a Champions League

Leave a comment