Real Madrid ta dauki La Liga na 2023/24

Real Madrid ta dauki La Liga na bana na 36 jimilla, dukka da saura wasa hur-hudu a karkare kakar bana.

Kungiyar Santiago Bernabeu ta samu wannan damar bayan da ta doke Cadiz 3-0 ranar Asabar a wasan mako na 34.

A ranar Girona ta doke Barcelona 4-2 a wasan hamayya a babbar gasar tamaula ta Spain.

Hakan ya sa Real Madrid ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 87 da tazarar maki 13 tsakani da Girona ta biyu da kuma Barcelona ta uku mai maki 73.

Real din ta lashe wasa 27 da canjaras shida aka doke ta karawa daya, da cin kwallo 74 aka zura mata 22 a raga a kakar nan.

Kuma Real ta fara kakar bana da cin wasa biyar a jere, kuma a wasan mako na biyu ta dare kan teburin La Liga har zuwa mako na biyar.

Daga baya gurbin ya kubuce mata, amma daga baya ta koma matakin farko tun daga mako na 18 daga lokacin ba ta sauko ba har ta kai ta dauki La Liga na bana na 36 jimilla.

Real, wadda ta yi karawa 18 kwallo bai shiga ragarta ba ta yi fama da ‘yan wasan da suka yi jinya, musamman Thibaut Courtois da David Alaba, sai dai Courtois ya buga wasan ranar Asabar a karon farko bayan jinyar wata tara.

Jude Bellingham ne na biyu a yawan cin kwallaye a La Liga mai 18 a raga, bayan Artem Dovbyk na Girona mai 20 a raga.

Vinicius Junior ne na biyu a yawan cin kwallaye a bana a La Liga a Real Madrid, mai 13 a raga, wanda ya bayar da 13 aka kuma zura a raga a gasar.

Wannan shi ne La Liga na biyu da Carlo Ancelotti ya lashe a Spain, amma na 12 jimilla a matakin kociyan kungiyar.

Dan kasar Italy shi ne keda tarihin lashe babban kofin gasar Spain, La Liga da na England, Premier League da na Italy, Serie A da na Germany Bundesliga da kuma na France, Ligue 1.

Ranar Laraba Real Madrid za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasa na biyu a Champions League karawar daf da karshe, bayan da suka tashi 2-2 a Germany ranar Talata.

Leave a comment