Real Madrid na shirin karbar bakuncin Bayern Munich

Ranar Laraba Real Madrid za ta karbi bakuncin Bayern Munich a wasa na biyu zagayen daf da karshe a Champions League.

A wasan farko da suka kara ranar Talata inda Bayern ta karbi bakuncin Real a Allianz Arena, sun tashi 2-2 a Germany.

Real wadda ta lashe La Liga na 36 jimilla ranar Asabar, bayan da Girona ta doke Barcelona 4-2, na fatan daukar Champions League na 15 jimilla.

Bayern Munich, wadda ta take da kofin zakarun Turai shida, za ta kare kakar bana ba tare da daukar kofi koda na shayi ba, bayan da Bayern Leverkusen ta dauki Bundesliga a karon farko a tarihinta na shekara 120.

‘Yan wasan Real sun fara atisaye a rufaffen daki daga baya suka fito fili, inda suka yi wasa da kwallo, daga baya aka raba filin gida biyu aka raba tamaula tsakanin wadanda suka buga karawar da ta doke Cadiz a La Liga ranar Asabar.

Leave a comment