Real Madrid na shirin karawa da Real Betis

Real Madrid na ci gaba da shirye-shiryen karawa da Real Betis a wasan mako na 16 a LaLiga ranar Asabar.

‘Yan wasan kungiyar sun motsa jiki, sun yi wasa da tamaula da guje-guje, sannan suka raba filin biyu suka taka leda.

Sun kammala atisayen da buga wa gola kwallo har da bugun fenariti.

Tchouameni da Vini Jr. wadanda ke kokarin murmurewa sun yi atisayensu a waje, amma ba a cikin ‘yan was aba.

Har yanzu Arda Güler na jinya, yayin da Courtois da Militao da Camavinga da Carvajal ke ta kokarin murmurwa.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara, Inda Real Madrid ta ci 2-1 a gidanta ranar 3 ga watan Satumbar 2022.

Da aka je gidan Betis sai suka tashi 0-0 ranar 5 ga watan Maris din 2023.

Real Madrid ce ta daya a kan teburin La Liga mai maki 38, iri daya da na Girona ta biyu.

Barcelona ce ta uku mai maki 34 da Atletico Madrid mai maki 31 ta hudu, ita kuwa Real Betis tana ta bakwai da maki 25.

Leave a comment