Real Madrid na shirin fuskantar Braga

Real Madrid za ta karbi bakuncin Braga a wasa na hurhudu a rukuni na Champions League da za ta buga a Santiago Bernabeu.

Ranar 24 ga watan Oktoba, Real Madrid ta je ta ci Sporting Braga 2-1 a wasa na uku-uku a cikin rukuni na uku a gasar ta zakarun Turai.

Real Madrid ce ta daya a teburin rukuni na uku, wadda ta ci wasa uku da maki tara, sai Napoli Napoli mai shida da Sporting Braga mai uku da kuma Union Berling mara maki.

Bayan da Real ta tashi ba ci a La Liga a gida da Rayo Vallecano ta yi atisaye a rufaffen daki daga nan ta fito filin wasa ta motsa jiki.

‘Yan wasa sun yi guje-guje da kwallo, sannan sun yi bani in baka, sannan suka raba kansu zuwa rukunai daga nan aka dunga gwada mai tsaron raga.

Jude Bellingham mai kwallo 10 a raga a gasar La Liga ta bana, ya motsa jiki a rufafen daki.

Leave a comment