Real da Man City da Man United da Arsenal na rububin Frimpong

Jeremie Frimpong na daf da barin Beyer Leverkusen a karshen kakar nan, yayin da Real Madrid da Manchester City da Arsenal da kuma Manchester United ke fatan daukar dan kwallon, wanda yake da kunshin yarjejeyar £35m ga duk wadda ke son daukarsa. (Bild – in German – subscription required)

Arsenal da Manchester City sun tuntubi Newcastle United kan sayen Bruno Guimaraes da zarar an kammala kakar bana, suna kuma fatan daya daga ciki za ta mallake shi. (Caughtoffside)

Kociyan Feyenoord, Arne Slot na shirin nada mataimakinsa, Sipke Hulshoff cikin na farko da zai yi aiki da shi a Liverpool da zarar ya maye gurbin Jurgen Klopp. (ESPN)

Wolves na shirin yi wa Gary O’Neil tayin kwantiragin kaka uku domin ya ci gaba da jan ragamar kungiyar (i Sport – subscription required)

Juventus na shirin rabuwa da kociyanta Massimiliano Allegri idan an kammala kakar bana (Rudy Galetti)

Bayern Munich za ta yi zawarcin kyaftin din Manchester United, Bruno Fernandes idan an kammala kakar nan, za ta yi haka ne saboda rashin kokarin da United ke fuskanta.(Independent)

Fitattun ‘yan wasan Bayern Munich ciki har da Harry Kane, na yin kiraye-kiraye da cewar koci,Thomas Tuchel ya sauya shawarar da ya yanke ta ajiye aikin a karshen kakar nan, ya ci gaba da jan ragamar kungiyar. (Abendzeitung – in German)

Napoli ta yi wa Antonio Conte tayin £5.6m duk shekara, bayan da AC Milan ta yi sanyi wajen batun son daukar kociyan. (Sport Italia via Football Italia)

Liverpool ta samu damar daukar dan kwallon Nice, Khephren Thuram kan £13m a karshen kakar nan. (Mirror)

Leave a comment