RB Leipzig ta janye daga zawarcin Sancho na Man United

Wasu rahotanni na cewa RB Leipzig ta janye daga kokarin daukar dan wasan Manchester United, Jadon Sancho.

Dan kwallon tawagar Ingila baya buga wasanni kusan wata uku da rabi, bayan rashin jituwa tsakaninsa da Erik ten Hag.

Rabon da ya buga tamaula tun wasan da Arsenal ta doke Manchester United cikin watan Satumba.

Mai shekara 23 ya taka rawar gani a Borussia Dortmund, hakan ya sa Leipzig take ganin yana da gudunmuwar da zai bayar a kungiyar.

Dan kwallon na karbar £350,000 a duk mako, kenan ba kowacce kungiya ce za ta iya daukar dan wasan ba, sai dai ya je wasannin aro.

United za ta iya bayar da aronsa a kungiyar waje banda wadda take Ingila, kenan zai iya barin Old Trafford a Janairu amma ba tabbas.

Kungiyar Juventus, wadda ake cewar na son sayen Sancho ta nisanta kanta da batun.

Itama Barcelona ta ce ba ta yi tunanin daukar dan wasan ba a Janairu, babu kuma cewa zai koma Saudi Arabia da taka leda.

Sancho dan wasa ne da ya yi daraja a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a lokacin da yake taka leda a Dortmund.

Dan wasan tawagar Ingila yana da hannu a cin kwallo 114 a wasa 137, wanda ya ci 50 daga ciki da bayar da 64 aka zura a raga a lokacin da yake taka leda a Jamus.

To sai dai mai shekara 23 ya ci kwallo 12 ya bayar da shida aka zura a raga a wasa 82 a Man United.

Kuma wasa uku ya buga a matakin canjin dan kwallo a kakar bana daga nan ya samu rashin jituwa da kociyan Man United.

Sancho yana da kunshin kwantiragi da Man United da zai kare a karshen kakar 2026 da cewar za a iya tsawaita masa kaka daya.

Leave a comment