RB Leipzig ta dauki Elmas daga Napoli

Kungiyar RB Leipzig mai buga Bundesliga ta sanar da daukar Eljif Elmas daga Napoli mai rike da Serie A na bara.

Mai shekara 24, zai koma Jamus da taka leda, bayan da Emil Forsberg, wanda ya koma kungiyar a 2015, wanda ya bayar da gudunmuwar da ta koma buga Bundesliga, yanzu New York Red Bulls ta dauke shi.

Lepzig, wadda take ta hudu a teburin Bundesliga a bana ta sanar cewar Elmas zai koma kungiyar daga 2 ga watan Janairun 2024, wanda ta dauka kan Yuro miliyan 23.

‘’Ya saka hannu kan kunshin yarjejeniyar kaka hudu, zai saka mana riga har zuwa karshen kakar 2028.’’ kamar yadda Leipzig ta sanar.

Elmas dan kwallon tawagar Arewacin Macedonia, ya koma Napoli da taka leda daga Fenerbahce a 2019, wanda ya buga wasa 143 Serie A, wanda ya lashe kofin a kakar da ta wuce.

‘’Yin wasa a Leipzig a gasar Bundesliga mafarki na ne ya zama gaskiya.’’ Kamar yadda Elmas ya fada a wani jawabi.

Leave a comment