RB Leipzig na son ta mayar da martabarta a Etihad

Marco Rose ya ce RB Leipzig za ta yi kokarin mayar da martabarta a Manchester City ranar Talata.

City za ta karbi bakuncin kungiyar Jamus a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni a Champions League.

Wannan shi ne karo na shida da za su kece raini a tsakaninsu, inda City ta ci uku da canajaras daya, Leipzig ta ci wasa daya.

Cikin watan Oktoba, City ta doke Leipzig 3-1 a Jamus a karawa ta bibiyu a cikin rukuni na bakwai.

City mai rike da kofin bara tana ta daya a kan teburi da maki 12, ita kuwa Leipzig mai maki tara tana ta biyu.

Dukkan kungiyoyin sun kai zagaye na biyu a gasar, illa dai ana son tantance wadda za ta yi ta farko da ta biyu a rukunin.

Daya wasan rukuni na bakwai da za a buga ranar Talata shi ne tsakanin Young Boys da Crvena Zvezda, wadanda kowacce take da maki daya.

A cikin watan Maris ne City ta doke Leipzig 7-0 a Etihad a zagayen ‘yan kungiyoyi 16 a gasar ta zakarun Turai.

A karawar ce Erling Haaland ya zura kwallo biyar a ragar kungiyar da ke buga Bundesliga.

Wasannin da za a buga ranar Talata:

  • Lazio da Celtic
  • Shakhtar Donetsk da Royal Antwerp
  • Manchester City da RB Leipzig       
  • AC Milan da Borussia Dortmund
  • Feyenoord da Atletico Madrid       
  • FC Barcelona da FC Porto       
  • Paris Saint-Germain da Newcastle United        
  • Young Boys da Crvena Zvezda

Leave a comment