Rashford yana cin Chelsea a wasa da Man United

Manchester United da Chelsea za su kara a wasan mako na 15 a Premier League ranar Laraba a Old Trafford.

Marcus Rashford bai taka rawar gani a wasan da United ta yi rashin nasara a Newcastle United da ci 1-0 ranar Asabar ba.

Tuni dai wasu ke ta kiraye-kirayen a ajiye shi daga tawagar England, wadda za ta buga Euro 2022 a Jamus.

Rashford, mai shekara 26, ya ci kwallo biyu a wasa 18 da ya yiwa United a kakar nan.

Dan wsan tawagar Ingila ya fuskanci Chelsea sau 17 da yin nasara biyar da canjaras bakwai da rashin nasara biyar.

Cikin wasannin, Rashford ya ci kwallo shida ya bayar da uku aka zura a raga.

Cikin wasa 17 daga 12 a Premier aka kara da Rashford a Man United da Chelsea, inda aka ci wasa uku da canjaras bakwai da rashin nasara biyu da shi.

A kuma wasannin ne Rashford ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da biyu aka zura a raga.

Rashford ya fuskanci Chelsea a wasa hudu a FA Cup, wanda aka yi nasara daya da shi aka doke su wasa uku, wanda bai ci kwallo ba, ya bayar da daya aka zura a raga.

To amma a League Cup shi ne ya ci biyun da Man United ta doke Chelsea 2-1 a zagaye na hudu a 2019-20.

Dan wasan Man United yana cikin wasan da Chelsea ta ci 1-0 a karawar karshe a FA Cup a 2018 da kuma 3-1 da Chelsea ta yi nasara a daf da karshe a 2019-20.

Leave a comment