Bidiyo: Ramadan ya sha da kyar a damben gwamnan Kano

Ramadan Garba Ramadan ya kai zagaye na biyu da kyar da gumin gushi a damben gwamman Kano ranar Alhamis, bayan da ya kasa buge Bahagon Sama’ila a Ado Bayero Square.

Wannan shi ne wasan farko da Ramadan dan damben Jamus ya yi tun bayan kammala azumi, wanda aka yi hutun dambe na kwanakin da aka yi azumi.

Damben ya bai wa mutane mamaki ganin da Ramadan ya kasa doke Bahagon Sama’ila daga Kudu, wanda tun farko ‘Yar Mage daga Kudu ya doke Shagon Audu Argungu daga Arewa.

Tun ana sa ran Ramadan zai buge Bahagon Sama’ila a turmin farko sai da suka yi fafatawar zagaye uku, sannan aka watsa yes ko no, inda Ramadan ya yi nasara.

Ranar Juma’a za a fafata tsakanin Garkuwan Dutse daga Kudu da kuma Dan Bichi daga Arewa.

Sakamakon wasannin da aka buga ranar Alhamis a damben gwamnan jihar Kano

  • Autan ZY daga Arewa ya kai zagayen gaba a kan Shagon Bahagon Kawoji Guramada
  • Autan Ali daga Jamus ya yi nasara a kan Shagon Habu Cingam daga Kudu
  • ‘Yar Mage daga Kudu ya doke Shagon Audu Argungu daga Arewa
  • Shamsun Autan Dan Bunza ya kai zagayen gaba a kan Inuwa Shagon Mai maciji

Leave a comment