Rafli Brych ya kafa tarihi a Bundesliga amma ya ji ciwo

Alkalin wasan tamaula, Felix Brych ya ji rauni a lokacin da yake busa wasa a Bundesliga ranar Asabar.

Brych ya yi alkalancin babbar gasar tamaula ta Jamus karo na 344 a fafatawar da Stuttgard ta ci Eintracht Frankfurt 2-1.

Kenan ya yi kan-kan-kan da tarihin Wolfgang Stark, wanda shima ya hura wasa 344 a Bundesliga.

Kamar yadda wata jaridar Jamus, DFB ta wallafa, ta ce Brych zai je a auna koshin lafiyarsa.

Alkalin ya zame ya fadi a minti na 32 ana tsaka da wasa, wanda ya gurde kafar hagu.

Likitoci sun duba shi an kuma daure kafar da bandeji, wanda ya ci gaba da jan ragama zuwa hutu.

Bayan da aka yi hutu ne ya bai wa mai jiran ko-ta-kwana, Patrick Schwengers usur, wanda ya ci gaba da aikin.

Sai dai rafling ya ce ya ji dadin bajintar yawan busa gasar Bundesliga da ya yi, amma gashi ba lafiya, yana cike da murna.

Leave a comment