Raducanu ta kai quarter final a Stuttgart Open

Emma Raducanu ta caskara Linda Noskova ta kuma kai quarter finals a gasar kwallon tennis ta Stuttgart Open.

Raducanu ta yi nasara da cin 6-0 ,7-5 cikin minti 81, mai shekara 21 za ta fuskanci mai rike da kofin Igwa Swantek, wadda ta yi waje da Elise Mertens da cin 6-3, 6-4.

Shima Cameron Norrie ya kai daf da na kusa da na karshe, amma a Barcelona Open bayan doke Roberto Bautista Agut da cin 6-4 6-3 – wasa na 200 da ya yi nasara a kwallon tennis kenan.

Ya kuma kai zagayen gaba cikin awa daya da minti 24 zai kuma fuskanci Tomas Etcheverry.

Leave a comment