Qatar ta kori kociyanta Carlos Queiroz

Hukumar kwallon kafa ta Qatar ta sanar da korar kociyanta Carlos Queiroz ranar Laraba.

Tuni kuma ta maye gurbinsa da dan kasar Spain, Tintin Marquez, ba ta kuma sanar da dalin korar kocin ba.

An bai wa Queiroz aikin a cikin watan Fabrairu kan yarjejeniyar kaka hudu da cewar zai kai kasar gasar kofin duniya a 2026.

An nada shi koci, bayan da Qatar ta kasa taka rawar gani a gasar kofin duniya da ta karbi bakunci a 2022, karkashin Felix Sanchez.

Tsohon kociyan Real Madrid da tawagar Portugal ya ja ragamar Qatar ta ci wasa biyu a karawar neman shiga gasar kofin duniya ta 2026.

Qatar ta casa India 3-0 da cascara Afghanistan 8-1 a wasannin neman shiga gasar ta kofin duniya.

A wasa 12 da ya ja ragamar Qatar, ya ci wasa biyar da canjaras biyu aka doke shi biyar.

Leave a comment