PSG ta lashe Ligue 1 na kakar nan 2023/24

Paris St German ta dauki Ligue 1 na bana na 12 jimilla, bayan da Monaco ta biyun teburi ta yi rashin nasara da ci 3-2 a hannun Lyon ranar Lahadi.

Kenan PSG wadda take ta daya a kan teburi da tazarar maki 13 ba kungiyar da za ta kamota a maki, bayan da saura wasa uku a karkare kakar nan.

Tun ranar Asabar ya kamata PSG ta dauki kofin bana, amma sai ta tashi 3-3 da Le Havre a gida, hakan ya sa sai a ranar Lahadi ta samu daukar Ligue 1.

Haka kuma kofi na 10 kenan PSG ta samu ta dauka daga kaka 10 a Ligue 1, wadda ke fatan lashe Champions League na kakar nan.

PSG za ta fafata da Borussia Dortmund a watan Mayu gida da waje a zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai.

https://twitter.com/PSG_English/status/1784660811371175955

Leave a comment