Paris Saint-Germain (PSG) ta nemi a É—age wasanta da Lens a gasar Ligue 1, domin ta samu damar shirya fuskantar Liverpool a gasar Champions League.
Kafin wannan, PSG za ta karɓi bakuncin Toulouse a gida ranar Juma’a 3 ga watan Afirilu, sannan kuma ta fuskanci Liverpool a zagayen kwata fainal na gasar zakarun Turai.
PSG da Liverpool za su fafata a zagaye na gaba na Champions League, inda a baya ƙungiyar Faransa ta taɓa fitar da ta Ingila a wani mataki na gasar.
An tsara cewa PSG za ta je gidan Lens ranar Asabar 11 ga watan Afirilu a Ligue 1, kwanaki uku kacal bayan karawar farko da Liverpool, sannan kuma za ta je Ingila domin wasa na biyu a filin Anfield bayan wasu kwanaki kaÉ—an.
Wannan cunkoson jadawalin ne ya sa PSG ta nemi a É—age wasan, domin ta samu nutsuwar shirya manyan wasanninta na Turai da kuma na cikin gida.
Sai dai ƙungiyar Lens ta yi watsi da wannan buƙata, inda ta bayyana cewa ya kamata a buga wasan kamar yadda aka tsara, domin kauce wa cunkoson jadawalin daga baya.
A nata ɓangaren, Liverpool za ta buga wasa da Fulham a gasar Premier League a ranar Asabar 11 ga watan Afirilu.
A halin yanzu, PSG ce ke jan ragamar teburin Ligue 1, inda take da tazarar maki É—aya kacal tsakaninta da Lens.
Kocin Lens, Pierre Sage, ya bayyana bayan nasarar da suka samu kan Angers da ci 5-1 cewa ba su da niyyar amincewa da É—age wasan da PSG ta nema.
A baya ma, PSG ta taɓa neman sauya ranar wasa da Nantes domin shirya wasanta na Champions League, wanda hakan ya taimaka mata kai wa zagaye na gaba.