PSG na daf da lashe Ligue 1 na 12 jimilla bayan doke Lorient

Ousmane Dembele da Kylian Mbappe kowanne ya ci kwallo bibiyu a wasan da Paris St-Germain ke daf da daukar Ligue 1, bayan cin Lorient 4-1 ranar Laraba.

PSG za ta jira mako na gaba ta lashe babban kofin gasar France na bana na uku a jere, bayan da Monaco ta yi nasara a kan Lille 1-0, inda Youssouf Fofana ya ci mata kwallon.

Tun kan su je hutu ne, PSG ta fara zura kwallo ta hannun Dembele a minti na 19, sannan Mbappe ya kara na biyu uku tsakani.

Haka kuma Mbappe ne ya bai wa Dembele kwallon da ya ci na biyu, wanda ya buga ta wuce tsakiyar kafafun Nathaniel Adjei daga baya kyaftin din tawagar France ya ci na biyu daf da za a tashi wasan.

Kwallon da Mbappe ya ci ya zama dan kasar France na farko da ya ci kwallo 25 ko fiye da kaka a Ligue 1 a kaka hudu tsakanin manyan gasar lik ta Turai biyar.

A zagaye na biyu ne mai masaukin baki, Bamba Dieng ya zare daya daga karawar ta ranar Laraba.

Tun a ranar Larabar ya kamata a bai wa PSG kofin bana, amma cin wasa da Monaco ta yi ya sa za a jira sai ranar Asabar idan ta doke Le Havre ta dauki Ligie 1 na 12 jimilla.

A karshen kakar nan Mbappe zai koma Real Madrid, bayan da PSG ta amince da hakan, wadda a baya ta hana dan wasan tafiya.

Tun a baya Mbappe ya sp ya koma Santiago Bernabeu da taka leda, amma sai ya tsawaita zamansa a PSG kafin gasar kofin duniya a Qatar.

Leave a comment