Premier League: Za a fafata tsakanin Arsenal da Chelsea

Arsenal da Chelsea za su fafata a kwantan Premier League karawar hamayya ranar Talata a Emirates.

Sun fafata a wasan farko ranar Asabar 21 ga watan Oktoban 2023 a Stamford Bridge, inda suka tashi 2-2.

Arsenal tana ta daya a kan teburin Premier League da maki 74, iri daya da na Liverpool ta biyu, amma da tazarar rarar kwallaye a tsakaninsu.

Ita kuwa Chelsea tana ta tara a teburin da maki 47 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wasa daya Chelsea ta ci daga fafata wa tara a dukkan fafatawa a Emirates, shi ne 2-0 a Agustan 2021.

Chelsea na daf da shan kashi a wasa biyu a jere a waje a Premier League a karawa da Arsenal a karon farko, tun bayan ukun da aka doke ta a Highbury tsakanin 2001 zuwa 2003.

Kungiyar Arsenal

Gunners ta lashe wasa 12 daga 16 da ta fafata a gida a Premier League a kakar nan, amma tana fuskantar barazanar rashin nasara biyu a jere a karon farko bayan shekara biyu.

Arsenal ta ci wasa 11 daga 13 da ta yi a 2024 da canjaras daya aka doke ta wasa daya.

Arsenal ta yi karawa 15 kwallo bai shiga ragarta ba, karin wasa biyar fiye da sauran kakar da ta kara kenan.

Kungiyar Chelsea

Ba a doke Chelsea a fafata wa takwas baya ba a Premier League da cin hudu da canjaras hudu da zura kwallo akalla biyu daga karawa shida.

Tana fatan yin wasa biyu a jere ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba a karon farko, tun wasa ukun da ta buga a Janairu zuwa Fabrairu 2023.

An zura kwallo 27 a ragar Chelsea a Premier League a wasannin waje, kaka da aka zura mata kwallaye da yawa tun bayan 15 da suka shiga ragarta a karawar waje a 1990/91.

Kuma kawo yanzu an zura kwallo 52 a ragar Chelsea a lik, an samu karin biyar kan yawan wadanda suka shiga ragarta a 2022/23.

Ta yi canjaras uku a jere a wasan waje a Premier League a karon farko tun bayan Satumbar 2000.

Mauricio Pochettino bai taba yin nasara ba a gidan Arsenal, wanda ya yi canjaras hudu aka doke shi uku a wasa bakwai da ya je Emirates tare da Southampton da kuma Tottenham.

Leave a comment