Premier League: Aston Villa da Sheffield United

Za a ci gaba da wasan mako na 18 a Premier League tsakanin Aston Villa da Sheffield United a daren Juma’a..

Sheffield, wadda a bana ta koma buga babbar gasar tamaula ta Ingila, itace ta karshen teburi ta 20 da maki takwas.

Aston Villa wadda ake mamakin rawar da take takawa a gasar zakarun Turai da ta Premier League a bana, tana ta uku da maki 38, iri daya da na Arsenal ta biyu da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta farko.

A jiya ne aka tashi kunnen doki 1-1 tsakanin Crystal Palace da Brighton a Selhurst Park.

Leave a comment